30 Satumba 2020 - 11:33
​Amurka: Trump Da Biden Sun Tafka Zazzafar Muhawara

A daren jiya ne aka tafka muhawara tsakanin shugaban kasar Amurka Donald Trump da kuma dan takarar shugabancin kasar karkashin inuwar jam’iyyar democrat Joe Biden.

ABNA24 : Muhawarar wadda aka tafka tsawon mintuna 90, wadda kuma aka watsa kai tsaye a kafofin yada labarai na Amurka da ma na duniya, ta nuna yadda mutanen biyu suka yi ta sukar junansu da kuma fallasa kansu.

A bisa ga yadda muhawarar ta gudana, Trump ya kasance a mai kare kansa ne bisa tuhumce-tuhumce a mafi yawan lokacin muhawarar, yayin da shi kuma Biden ya kasance mai kai farmaki a kan Trump.

Muhawarar ta tabo bangarori daban-daban, da suka hada da shirin Obama na kiwon lafiya, da kuma batun maye gurbin bababr alkaliya da ta mutu a babbar kotun kolin kasar.

Dangane da batun Corona, Biden ya caccaki Trump tare da bayyana shi a matsatin wada ya yi sakaci har cutar ta yi wa Amurkawa babbar illa tare da lakume rayukansu, yayin da shi kuma Trump ya dora alhakin a kan kasar China.

Baya ga haka kuma Biden ya bayyana Trump a matsayin wanda ya kara ruruta wutar rikicin wariyar launin fata da ake nuna ma bakaken fata akasar Amurka, musamman bayan kisan George Floyd, inda Trump ya rika sukar masu zanga-zanga tare da kiransu a matsayin ‘yan daba ‘yan ta’adda, yayin da shi kuma Trump ya kare kansa da cewa, zanga-zangar ba ta zaman lafiya ba ce.

Kamar yadda kuma Biden ya bayyana Trump a matsayin babban makaryaci, wanda kowa ya san shi a haka a duk duniya.

342/